1. MAI WA ‘AZI —
WATSON GOODMAN
KYAUTA—KADA A SAYAR
TAIMAKO DAGA SAMA
‘TAIMAKO DAGA SAMA’ An gyara shi kanana ne don ka yi
anfani da shi lokacin da kana jiran wani kokuwa a kan tafiya.
Kada ka battadda wannan lokaci; amma ka bada abinci ma
ruhunka.
Na yi kokari in mai da rubutu babba da kuma saukin
karatu. An debo kan magana daga wurare dabban dabban
daga Litafi Mai Tsarki don na ba da gaskiya Litafi Mai
Tsarkine yafi duka. Ina zato za mu fahinta Maganar Allah
wanda ya ba mu a Litafi Mai Tsarki.
Kalman Allah ya sauko daga sama da kuma zai taimake
zuciyar wanda ya karbe shi. In mutum ya tuba ya bar zunubi;
ya bada gaskiya ga Mai Ceto; Yesu Almasihu, da dukan zuci-
yar shi, Allah zai ba shi murna da kwanciyar rai. Na gane
ma’anar wannan a 1937, da dukan shekarun da suka biyo na
sani ina tare da Ubangiji. Ina rokonka ka karbe Shi yanzu, in
ba ka rigaya ba karbe shi ba. —Watson Goodman(1920-2002)