SlideShare a Scribd company logo
1 of 3
Download to read offline
Wasikar Jagora Imam Khamenei Ga Matasan Kasashen Turai Da Arewacin
Amurka
21/01/2015
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Zuwa Ga Dukkanin Matasan Kasashen Turai Da Arewacin Amurka
Lamurrann baya-bayan nan da suka faru a kasar
Faransa da makamantansu a wasu kasashen
Yammaci, su ne suka sanya ni ganin ya dace in yi
magana da ku kai tsaye. Ina magana da ku ne, Ya
ku matasa; ba wai saboda na raina iyayenku ba,
face dai sai saboda ku ne manyan gobe, wadanda
makomar al'umma da kuma kasarku take
hannunsu; sannan kuma saboda ina ganin
zukatanku cike suke da neman sanin gaskiya.
Haka nan kuma ba wai ina magana ne da ‘yan
siyasa da jami'an gwamnatocinku ba ne, don kuwa
na yi amanna da cewa da gangan sannan kuma da saninsu suka kawar da siyasarsu daga tafarkin
gaskiya da hakika.
Magana ta da ku kan Musulunci ne, musamman ma dangane irin abin da ake gabatar muku da shi
a matsayin Musuluncin.
Tsawon shekaru ashirin din da suka gabata zuwa sama - wato tun daga lokacin rugujewar
Tarayyar Sobiyeti - an gudanar da gagarumin kokarin bayyanar da wannan addini mai girma a
matsayin wani gagarumin abin tsoro. Abin bakin cikin shi ne cewa irin wannan yanayi na sanya
tsoro da kyamar (wannan addini) wani lamari ne mai tsoron tarihi cikin tarihin siyasar kasashen
yammaci.
Ni dai a nan ba ina so ne in yi magana dangane da ‘irin kyama da tsoratarwa' daban-daban da ya
zuwa yanzu aka sanya cikin zukatan al'ummomin kasashen yammaci ba. Idan kuka koma kadan
cikin tarihi, za ku ga cewa sabbin marubuta tarihi, sun soki mu'amalar rashin adalci da gaskiya
da gwamnatocin yammaci suka yi wa al'ummomi da al'adun duniya. Tarihin Turai da Amurka ya
rusunar da kansa cikin kunya saboda bautar da mutane, mulkin mallaka da kuma zaluntar
wadanda ba fararen fata da kuma wadanda ba Kiristoci ba da suka yi. Masana da malaman
tarihinku suna cikin kunyar irin zubar da jinin da aka yi da sunan addini tsakanin mabiya darikar
Katolika da Protestant ko kuma da sunan ‘yan kasanci da kabilanci a yakukuwan duniya na daya
da na biyu. Shi kansa hakan wani abin jinjinawa ne.
Manufar bijiro da wani bangare na wannan doguwar fehrisa na abubuwan da suka faru, ba ita ce
sukar tarihi ba, face dai abin da nake so shi ne ku tambayi masananku shin me ya sa a koda
yaushe sai bayan jinkiri na gomomin shekaru ko kuma ma daruruwan shekaru ne lamirin
al'ummomin yammaci ya ke farkawa da kuma dawowa cikin hayacinsa? Me ya sa ake damfara
lamirin mutane ga abubuwan da suka faru cikin tarihin shekaru aru aru ba batutuwan da suke
faruwa a halin yanzu ba? Me ya sa ake kange mutane daga fahimtar lamurra masu muhimmanci
irin su hanyoyin mu'amala da al'adu da kuma tunani na Musulunci?
Ku da kanku kun san cewa wulakanci da haifar da kiyayya da kirkirar tsoron sauran mutane na
boge, suna a matsayin wani fage ne da aka yi tarayya cikinsa wajen haifar da dukkanin irin
wadannan zalunci da mummunan amfani da mutane. A halin yanzu ina son tambayarku, shin me
ya sa yanzu aka dawo da tsohuwar siyasar sanya tsoro da kyamar Musulunci da musulmi? Me ya
sa tsarin mulki na duniya a halin yanzu ya sanya tunani na Musulunci a gaba? Shin wasu
abubuwa ne da suke cikin tunani da koyarwar Musulunci da har zai zamanto kafar ungulu ga
tsare-tsare da siyasar manyan kasashen duniya, sannan kuma me za su samu wajen bakanta
fuskar Musulunci?
A saboda haka, bukata ta ta farko ita ce ku yi tambaya da kuma binciko dalilin irin wannan
gagarumin kokari na bata sunan Musulunci.
Bukata ta ta biyu, ita ce yayin mayar da martani ga irin wannan gagarumin bakar farfagandar
bata sunan Musulunci (da ake yi), ku yi kokarin fahimtar wannan addini (Musulunci) da
koyarwar ta hakika kai tsaye. Lafiyayyen hankali yana hukumta wajibcin sanin hakikanin abin da
ake tsoratar da ku shi da kuma nesanta ku daga gare shi. Ni dai ba ina cewa ne lalle sai kun yarda
da fahimta ta ko fahimtar wani kan Musulunci ba, sai dai abin da nake cewa shi ne kada ku bari a
kange ku daga wannan hakikar wacce take da tasiri cikin duniyar yau saboda cimma wata bakar
manufa. Kada ku bari cikin riya su gabatar muku da ‘yan ta'addan da suke karkashin ikonsu a
matsayin wakilan Musulunci. Kamata yayi ku fahimci Musulunci daga tushensa na asali. Ku
fahimci Musulunci ta hanyar Alkur'ani da rayuwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi da Alayensa).
A nan ina son in tambaye ku, shin ya zuwa yanzu kun taba karanta Alkur'anin musulmi kai
tsaye? Shin kun taba karantar koyarwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi da Alayensa) da kyawawan halaye da ‘yan'adamtakarsa? Shin ya zuwa yanzu kun
fahimci sakon Musulunci ta wata kafa ta daban, ba kafar watsa labarai ba? Shin kun taba
tambayar kanku ya ya aka yi wannan Musuluncin, sannan bisa wasu koyarwa ya samu daman
zama mafi girman al'adu da ci gaban ilimi da tunani na duniya sannan kuma ya tarbiyyantar da
mafi girma da kyawun masana da masu tunani na duniya?
Ina kiranku da kada ku bari a yi amfani da bakar siyasa da wauta wajen katange ku daga gaskiya,
da kuma kawar da yiyuwar yin alkalanci cikin adalci daga gare ku. A halin yanzu da kafafen
sadarwa suka rusa ganuwar kan iyakokin kasashe, kada ku bari a kange ku cikin kirkirarrun kan
iyakoki na boge. Duk da cewa babu wani mutum, a kan kansa, da zai cike wannan gibin da aka
samar, amma kowane guda daga cikinku zai iya samar da gadar tunani da adalci a kan wannan
gibin da aka haifar. Duk da cewa wannan kalubalen da aka kirkira tsakanin Musulunci da ku
matasa wani kalubale ne mai sarkakiyar gaske, to amma hakan yana iya kirkiro sabbin
tambayoyi cikin zukatanku da suke neman sanin hakika. Kokari wajen samo amsoshin wadannan
tambayoyi, zai samar muku da wata dama ta gano wasu sabbin gaskiyar.
A saboda haka, kada ku bari wannan dama ta fahimtar gaskiyar Musulunci ta kubuce muku, don
me yiyuwa ta hanyar wannan jin nauyi a jika da kuke da shi, al'ummomi masu zuwa za su rubuta
tarihin irin wannan mu'amala da kasashen yammaci suka yi da Musulunci cikin sauki ba tare da
wahala ba.
Sayyid Ali Khamenei
1/11/1393
(21/01/2015)

More Related Content

Viewers also liked

Poruka ajatollaha hameneija, lidera irana, svekolikoj omladini evrope i sj...
Poruka  ajatollaha hameneija,  lidera irana,  svekolikoj omladini evrope i sj...Poruka  ajatollaha hameneija,  lidera irana,  svekolikoj omladini evrope i sj...
Poruka ajatollaha hameneija, lidera irana, svekolikoj omladini evrope i sj...hajj2013
 
The holy quran sveti kur’an
The holy quran sveti kur’anThe holy quran sveti kur’an
The holy quran sveti kur’anhajj2013
 
The holy quran english translation of the meanings by abdullah yusuf
The holy quran english translation of the meanings by abdullah yusufThe holy quran english translation of the meanings by abdullah yusuf
The holy quran english translation of the meanings by abdullah yusufhajj2013
 
• Swahili
•  Swahili•  Swahili
• Swahilihajj2013
 
• Azərbaycan
•  Azərbaycan•  Azərbaycan
• Azərbaycanhajj2013
 
• Bosnian
•  Bosnian•  Bosnian
• Bosnianhajj2013
 
Viewers also liked (8)

Poruka ajatollaha hameneija, lidera irana, svekolikoj omladini evrope i sj...
Poruka  ajatollaha hameneija,  lidera irana,  svekolikoj omladini evrope i sj...Poruka  ajatollaha hameneija,  lidera irana,  svekolikoj omladini evrope i sj...
Poruka ajatollaha hameneija, lidera irana, svekolikoj omladini evrope i sj...
 
The holy quran sveti kur’an
The holy quran sveti kur’anThe holy quran sveti kur’an
The holy quran sveti kur’an
 
The holy quran english translation of the meanings by abdullah yusuf
The holy quran english translation of the meanings by abdullah yusufThe holy quran english translation of the meanings by abdullah yusuf
The holy quran english translation of the meanings by abdullah yusuf
 
• Swahili
•  Swahili•  Swahili
• Swahili
 
• Azərbaycan
•  Azərbaycan•  Azərbaycan
• Azərbaycan
 
• Hausa
•  Hausa•  Hausa
• Hausa
 
• Hausa
•  Hausa•  Hausa
• Hausa
 
• Bosnian
•  Bosnian•  Bosnian
• Bosnian
 
More from hajj2013

神聖なコーラン
神聖なコーラン神聖なコーラン
神聖なコーランhajj2013
 
신성한 크어랜
신성한 크어랜신성한 크어랜
신성한 크어랜hajj2013
 
The holy quran svet quran translation of the meanings in croatian prevođenje ...
The holy quran svet quran translation of the meanings in croatian prevođenje ...The holy quran svet quran translation of the meanings in croatian prevođenje ...
The holy quran svet quran translation of the meanings in croatian prevođenje ...hajj2013
 
Suci quran
Suci quranSuci quran
Suci quranhajj2013
 
Pyhä quran finnish
Pyhä quran  finnishPyhä quran  finnish
Pyhä quran finnishhajj2013
 
Helligst quran norwegian
Helligst quran  norwegianHelligst quran  norwegian
Helligst quran norwegianhajj2013
 
Helig quran översättning om mening
Helig quran översättning om meningHelig quran översättning om mening
Helig quran översättning om meninghajj2013
 
Esperanto holy quran
Esperanto holy quranEsperanto holy quran
Esperanto holy quranhajj2013
 
El quran santo (koran)interpretación española de los significados el ajustar ...
El quran santo (koran)interpretación española de los significados el ajustar ...El quran santo (koran)interpretación española de los significados el ajustar ...
El quran santo (koran)interpretación española de los significados el ajustar ...hajj2013
 
El quran santo(koran)
El quran santo(koran)El quran santo(koran)
El quran santo(koran)hajj2013
 
Quran ukrainian
Quran  ukrainianQuran  ukrainian
Quran ukrainianhajj2013
 
Dumnezeiesc quran romanian
Dumnezeiesc quran romanianDumnezeiesc quran romanian
Dumnezeiesc quran romanianhajj2013
 
The holy koran english translation of the meanings by mohammad marmaduke pick...
The holy koran english translation of the meanings by mohammad marmaduke pick...The holy koran english translation of the meanings by mohammad marmaduke pick...
The holy koran english translation of the meanings by mohammad marmaduke pick...hajj2013
 
śWięty quran noble kuran tłumaczenie od ten treści po polsku
śWięty quran noble kuran tłumaczenie od ten treści po polskuśWięty quran noble kuran tłumaczenie od ten treści po polsku
śWięty quran noble kuran tłumaczenie od ten treści po polskuhajj2013
 
Hellige quran translated by hadi abdollahian
Hellige quran translated by hadi abdollahianHellige quran translated by hadi abdollahian
Hellige quran translated by hadi abdollahianhajj2013
 
De heilig quran translated by hadi abdollahian
De heilig quran translated by hadi abdollahianDe heilig quran translated by hadi abdollahian
De heilig quran translated by hadi abdollahianhajj2013
 
欧米の若者に向けた最高指導者のメッセージ
欧米の若者に向けた最高指導者のメッセージ欧米の若者に向けた最高指導者のメッセージ
欧米の若者に向けた最高指導者のメッセージhajj2013
 
فرانس کے حالیہ واقعات کے بعد یورپ اور شمالی امریکی ملکوں کے نوجوانوں کے نام پ...
فرانس کے حالیہ واقعات کے بعد یورپ اور شمالی امریکی ملکوں کے نوجوانوں کے نام پ...فرانس کے حالیہ واقعات کے بعد یورپ اور شمالی امریکی ملکوں کے نوجوانوں کے نام پ...
فرانس کے حالیہ واقعات کے بعد یورپ اور شمالی امریکی ملکوں کے نوجوانوں کے نام پ...hajj2013
 
письмо великого лидера исламской революции молодежи европы и северной америки
письмо великого лидера исламской революции молодежи европы и северной америкиписьмо великого лидера исламской революции молодежи европы и северной америки
письмо великого лидера исламской революции молодежи европы и северной америкиhajj2013
 
Mensaje del gran líder los estudiantes en general de europa y norte américa
Mensaje del gran líder los estudiantes en general de europa y norte américaMensaje del gran líder los estudiantes en general de europa y norte américa
Mensaje del gran líder los estudiantes en general de europa y norte américahajj2013
 
More from hajj2013 (20)

神聖なコーラン
神聖なコーラン神聖なコーラン
神聖なコーラン
 
신성한 크어랜
신성한 크어랜신성한 크어랜
신성한 크어랜
 
The holy quran svet quran translation of the meanings in croatian prevođenje ...
The holy quran svet quran translation of the meanings in croatian prevođenje ...The holy quran svet quran translation of the meanings in croatian prevođenje ...
The holy quran svet quran translation of the meanings in croatian prevođenje ...
 
Suci quran
Suci quranSuci quran
Suci quran
 
Pyhä quran finnish
Pyhä quran  finnishPyhä quran  finnish
Pyhä quran finnish
 
Helligst quran norwegian
Helligst quran  norwegianHelligst quran  norwegian
Helligst quran norwegian
 
Helig quran översättning om mening
Helig quran översättning om meningHelig quran översättning om mening
Helig quran översättning om mening
 
Esperanto holy quran
Esperanto holy quranEsperanto holy quran
Esperanto holy quran
 
El quran santo (koran)interpretación española de los significados el ajustar ...
El quran santo (koran)interpretación española de los significados el ajustar ...El quran santo (koran)interpretación española de los significados el ajustar ...
El quran santo (koran)interpretación española de los significados el ajustar ...
 
El quran santo(koran)
El quran santo(koran)El quran santo(koran)
El quran santo(koran)
 
Quran ukrainian
Quran  ukrainianQuran  ukrainian
Quran ukrainian
 
Dumnezeiesc quran romanian
Dumnezeiesc quran romanianDumnezeiesc quran romanian
Dumnezeiesc quran romanian
 
The holy koran english translation of the meanings by mohammad marmaduke pick...
The holy koran english translation of the meanings by mohammad marmaduke pick...The holy koran english translation of the meanings by mohammad marmaduke pick...
The holy koran english translation of the meanings by mohammad marmaduke pick...
 
śWięty quran noble kuran tłumaczenie od ten treści po polsku
śWięty quran noble kuran tłumaczenie od ten treści po polskuśWięty quran noble kuran tłumaczenie od ten treści po polsku
śWięty quran noble kuran tłumaczenie od ten treści po polsku
 
Hellige quran translated by hadi abdollahian
Hellige quran translated by hadi abdollahianHellige quran translated by hadi abdollahian
Hellige quran translated by hadi abdollahian
 
De heilig quran translated by hadi abdollahian
De heilig quran translated by hadi abdollahianDe heilig quran translated by hadi abdollahian
De heilig quran translated by hadi abdollahian
 
欧米の若者に向けた最高指導者のメッセージ
欧米の若者に向けた最高指導者のメッセージ欧米の若者に向けた最高指導者のメッセージ
欧米の若者に向けた最高指導者のメッセージ
 
فرانس کے حالیہ واقعات کے بعد یورپ اور شمالی امریکی ملکوں کے نوجوانوں کے نام پ...
فرانس کے حالیہ واقعات کے بعد یورپ اور شمالی امریکی ملکوں کے نوجوانوں کے نام پ...فرانس کے حالیہ واقعات کے بعد یورپ اور شمالی امریکی ملکوں کے نوجوانوں کے نام پ...
فرانس کے حالیہ واقعات کے بعد یورپ اور شمالی امریکی ملکوں کے نوجوانوں کے نام پ...
 
письмо великого лидера исламской революции молодежи европы и северной америки
письмо великого лидера исламской революции молодежи европы и северной америкиписьмо великого лидера исламской революции молодежи европы и северной америки
письмо великого лидера исламской революции молодежи европы и северной америки
 
Mensaje del gran líder los estudiantes en general de europa y norte américa
Mensaje del gran líder los estudiantes en general de europa y norte américaMensaje del gran líder los estudiantes en general de europa y norte américa
Mensaje del gran líder los estudiantes en general de europa y norte américa
 
Wasikar jagora imam khamenei ga matasan kasashen turai da arewacin amurka

  • 1. Wasikar Jagora Imam Khamenei Ga Matasan Kasashen Turai Da Arewacin Amurka 21/01/2015 Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Zuwa Ga Dukkanin Matasan Kasashen Turai Da Arewacin Amurka Lamurrann baya-bayan nan da suka faru a kasar Faransa da makamantansu a wasu kasashen Yammaci, su ne suka sanya ni ganin ya dace in yi magana da ku kai tsaye. Ina magana da ku ne, Ya ku matasa; ba wai saboda na raina iyayenku ba, face dai sai saboda ku ne manyan gobe, wadanda makomar al'umma da kuma kasarku take hannunsu; sannan kuma saboda ina ganin zukatanku cike suke da neman sanin gaskiya. Haka nan kuma ba wai ina magana ne da ‘yan siyasa da jami'an gwamnatocinku ba ne, don kuwa na yi amanna da cewa da gangan sannan kuma da saninsu suka kawar da siyasarsu daga tafarkin gaskiya da hakika. Magana ta da ku kan Musulunci ne, musamman ma dangane irin abin da ake gabatar muku da shi a matsayin Musuluncin. Tsawon shekaru ashirin din da suka gabata zuwa sama - wato tun daga lokacin rugujewar Tarayyar Sobiyeti - an gudanar da gagarumin kokarin bayyanar da wannan addini mai girma a matsayin wani gagarumin abin tsoro. Abin bakin cikin shi ne cewa irin wannan yanayi na sanya tsoro da kyamar (wannan addini) wani lamari ne mai tsoron tarihi cikin tarihin siyasar kasashen yammaci. Ni dai a nan ba ina so ne in yi magana dangane da ‘irin kyama da tsoratarwa' daban-daban da ya zuwa yanzu aka sanya cikin zukatan al'ummomin kasashen yammaci ba. Idan kuka koma kadan cikin tarihi, za ku ga cewa sabbin marubuta tarihi, sun soki mu'amalar rashin adalci da gaskiya da gwamnatocin yammaci suka yi wa al'ummomi da al'adun duniya. Tarihin Turai da Amurka ya rusunar da kansa cikin kunya saboda bautar da mutane, mulkin mallaka da kuma zaluntar wadanda ba fararen fata da kuma wadanda ba Kiristoci ba da suka yi. Masana da malaman tarihinku suna cikin kunyar irin zubar da jinin da aka yi da sunan addini tsakanin mabiya darikar Katolika da Protestant ko kuma da sunan ‘yan kasanci da kabilanci a yakukuwan duniya na daya da na biyu. Shi kansa hakan wani abin jinjinawa ne. Manufar bijiro da wani bangare na wannan doguwar fehrisa na abubuwan da suka faru, ba ita ce sukar tarihi ba, face dai abin da nake so shi ne ku tambayi masananku shin me ya sa a koda yaushe sai bayan jinkiri na gomomin shekaru ko kuma ma daruruwan shekaru ne lamirin al'ummomin yammaci ya ke farkawa da kuma dawowa cikin hayacinsa? Me ya sa ake damfara lamirin mutane ga abubuwan da suka faru cikin tarihin shekaru aru aru ba batutuwan da suke faruwa a halin yanzu ba? Me ya sa ake kange mutane daga fahimtar lamurra masu muhimmanci
  • 2. irin su hanyoyin mu'amala da al'adu da kuma tunani na Musulunci? Ku da kanku kun san cewa wulakanci da haifar da kiyayya da kirkirar tsoron sauran mutane na boge, suna a matsayin wani fage ne da aka yi tarayya cikinsa wajen haifar da dukkanin irin wadannan zalunci da mummunan amfani da mutane. A halin yanzu ina son tambayarku, shin me ya sa yanzu aka dawo da tsohuwar siyasar sanya tsoro da kyamar Musulunci da musulmi? Me ya sa tsarin mulki na duniya a halin yanzu ya sanya tunani na Musulunci a gaba? Shin wasu abubuwa ne da suke cikin tunani da koyarwar Musulunci da har zai zamanto kafar ungulu ga tsare-tsare da siyasar manyan kasashen duniya, sannan kuma me za su samu wajen bakanta fuskar Musulunci? A saboda haka, bukata ta ta farko ita ce ku yi tambaya da kuma binciko dalilin irin wannan gagarumin kokari na bata sunan Musulunci. Bukata ta ta biyu, ita ce yayin mayar da martani ga irin wannan gagarumin bakar farfagandar bata sunan Musulunci (da ake yi), ku yi kokarin fahimtar wannan addini (Musulunci) da koyarwar ta hakika kai tsaye. Lafiyayyen hankali yana hukumta wajibcin sanin hakikanin abin da ake tsoratar da ku shi da kuma nesanta ku daga gare shi. Ni dai ba ina cewa ne lalle sai kun yarda da fahimta ta ko fahimtar wani kan Musulunci ba, sai dai abin da nake cewa shi ne kada ku bari a kange ku daga wannan hakikar wacce take da tasiri cikin duniyar yau saboda cimma wata bakar manufa. Kada ku bari cikin riya su gabatar muku da ‘yan ta'addan da suke karkashin ikonsu a matsayin wakilan Musulunci. Kamata yayi ku fahimci Musulunci daga tushensa na asali. Ku fahimci Musulunci ta hanyar Alkur'ani da rayuwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa). A nan ina son in tambaye ku, shin ya zuwa yanzu kun taba karanta Alkur'anin musulmi kai tsaye? Shin kun taba karantar koyarwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa) da kyawawan halaye da ‘yan'adamtakarsa? Shin ya zuwa yanzu kun fahimci sakon Musulunci ta wata kafa ta daban, ba kafar watsa labarai ba? Shin kun taba tambayar kanku ya ya aka yi wannan Musuluncin, sannan bisa wasu koyarwa ya samu daman zama mafi girman al'adu da ci gaban ilimi da tunani na duniya sannan kuma ya tarbiyyantar da mafi girma da kyawun masana da masu tunani na duniya? Ina kiranku da kada ku bari a yi amfani da bakar siyasa da wauta wajen katange ku daga gaskiya, da kuma kawar da yiyuwar yin alkalanci cikin adalci daga gare ku. A halin yanzu da kafafen sadarwa suka rusa ganuwar kan iyakokin kasashe, kada ku bari a kange ku cikin kirkirarrun kan iyakoki na boge. Duk da cewa babu wani mutum, a kan kansa, da zai cike wannan gibin da aka samar, amma kowane guda daga cikinku zai iya samar da gadar tunani da adalci a kan wannan gibin da aka haifar. Duk da cewa wannan kalubalen da aka kirkira tsakanin Musulunci da ku matasa wani kalubale ne mai sarkakiyar gaske, to amma hakan yana iya kirkiro sabbin tambayoyi cikin zukatanku da suke neman sanin hakika. Kokari wajen samo amsoshin wadannan tambayoyi, zai samar muku da wata dama ta gano wasu sabbin gaskiyar. A saboda haka, kada ku bari wannan dama ta fahimtar gaskiyar Musulunci ta kubuce muku, don me yiyuwa ta hanyar wannan jin nauyi a jika da kuke da shi, al'ummomi masu zuwa za su rubuta tarihin irin wannan mu'amala da kasashen yammaci suka yi da Musulunci cikin sauki ba tare da
  • 3. wahala ba. Sayyid Ali Khamenei 1/11/1393 (21/01/2015)